
Labaran Duniya
Allah ubangiji yajikanka yayi maka rahama yar adua kayi abun azo a gani a nigeria 🤲
Yar’Adua
“Ya Allah, Mai Rahama, Mai jin ƙai, muna roƙonka da zuciya ɗaya da cikakken tawali’u: Ka jikan bawanka Umaru Musa Yar’Adua. Ka gafarta masa kurakuransa na ɗan Adam. Ka azurta shi da kabari mai faɗi da haske. Ka sa aljanna ce makomarsa, Ka cika kabarinsa da ni’ima da dumin rahamarka.
Ya Allah, ka saka masa da alkhairi bisa kyawawan niyyarsa da ayyukan alheri da ya yi wa Najeriya da ‘yan ƙasa. Ka gafarta masa inda ya yi kuskure, ka sanya shi cikin sahun bayinka salihai. Ka hadamu da shi a aljanna Firdaus cikin rahamarka.
Ya Allah, ka albarkaci ‘ya’yansa da zuriyarsa, ka tabbatar da dawwamammen alkhairi a gare su. Ka azurta Najeriya da shugabannin masu koyi da gaskiyarsa, amincinsa, da tsoron Allah. Ameen.”