
Buhari mutum ne mai tsoron Allah inji mufti menk Allah yaji kansa yayi masa rahama
Buhari Mutum Ne Mai Tsoron Allah Da Kuma Son Addini, Inji Shiekh Mufti MenkDaga Muhammad Kwairi WaziriShahararren malamin addinin Musulunci daga ƙasar Zimbabwe, Sheikh Mufti Ismail Menk, ya bayyana tsohon shugaban ƙasa na Najeriya, Muhammadu Buhari, a matsayin mutum mai tsantsar ƙaunar addini da tsoron Allah.Malamin ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a yayin da ake ci gaba da tuna irin gudunmawar da Buhari ya bayar tun lokacin da yake mulki har zuwa bayan rasuwarsa. Ya ce Buhari ya kasance mutum mai tsayayyar akida, wanda ya yi ƙoƙari wajen ganin ya yi mulki bisa gaskiya da adalci.A cewar Mufti Menk, “Buhari mutum ne mai son addini. Ya kasance mai sauƙin kai, mai tsoron Allah, kuma mai ƙoƙarin ganin ya bar wata alama mai kyau ga ƙasarsa da al’ummarta.”Sheikh Menk ya ƙara da cewa irin wannan hali na ƙaunar addini da tsoron Allah yana daga cikin abubuwan da ke kawo albarka ga shugabanci, inda ya jaddada cewa dole ne a ci gaba da koyi da irin rayuwar gaskiya da Buhari ya yi ƙoƙarin nuna wa al’umma.Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya saka masa da aljanna, tare da jaddada cewa duniya na buƙatar shugabanni masu tsoron Allah da kishin talakawa kamar Muhammadu Buhari.Wannan kalamai na Sheikh Mufti Menk na ƙara tabbatar da yadda mutane daga sassa daban-daban na duniya ke nuna girmamawa da yabon halayen Buhari, musamman wajen tsayawa kan nagarta, tsoron Allah, da kishin ƙasa.