
Sojojin nigeria sunkama masu kaiwa yan bindiga makamai har jeji
Dakarun Sojojin Nigeria sun kama wasu manyan rikakkun ‘yan ta’adda masu safaran makaman ta’addanci zuwa ga barayin daji
An kamasu akan hanyar Sabon Birni na jihar Kaduna suna tafiya a cikin motarsu kirar Golf 4 mai launin baki, motar tana da register kamar haka: Abuja YAB 385 K7
Da aka bincika cikin motar an samu bindigogi kirar AK47 da harsashi kusan guda dari hudu, da wayoyi da kayan tsafi da kudade
Ga sunayen ‘yan ta’addan
(1) Yakubu Jilbril mai shekaru 45
(2) Abubakar Yahaya mai shekaru 45
(3) Isiyaku Sani mai shekaru 30
Sai dai zuwa yanzu muna kyautata zaton sun rigamu isa |ahira
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bada nasara aka ganosu ta yanda basu kai ga nasaran isar da makaman zuwa ga ‘yan ta’addan daji ba
Yaa Allah Ka cigaba da tona asirin ‘yan ta’adda a duk inda suka buya da masu taimakonsu ta kowace irin hanya